Sakamakon janyewar tasa, yanzu haka sakamakon zaben zai karkata ne ga ko dai shugaban jam'iyyar mai ci Kwabena Adjei, ko kuma babban jami'in hukumar kula da bala'u ta kasar Kofi Portuphy.
Kafin fara kada kuri'un dai sai da shugaban kasar ta Ghana John Dramani Mahama, ya ja hankalin wakilan jam'iyyar da su hada kai wuri guda, tare da magance rikicin cikin gida, dama kalubalen dake fuskantar jam'iyyar daga 'yan adawa. Ya ce hadin kan 'ya 'yan jam'iyyar ne kadai zai iya bata damar lashe zabubbuka, ta kuma samu zarafin ciyar da kasar gaba.
A halin yanzu dai jam'iyyar ta NDC ce ke rike da kujerun majalissar dokokin kasar 147 cikin 275, yayin da jam'iyyar adawa ta NPP ke da kujeru 121.