Ana kuma fatan wannan gasa za ta bada damar zakulo wadanda za su wakilci kasar, a gasar wasannin motsa jiki ta nahiyar Afirka ta shekarar 2015 wadda za a yi a kasar Congo Brazzaville, da kuma gasar Olamfik ta 2016 da za a yi a birnin Rio na kasar Brazil.
Da yake jawabi ya yin bikin bude gasar, ministan ma'aikatar harkokin matasa da wasannin kasar Mahama Ayariga, cewa ya yi hukumar wasannin kasar na da burin ganin an samar da karin damar shigar nakasassu cikin harkokin wasanni, baya ga kokarin da ake yi na kafa wani asusu na bunkasa wasanni ga ajin masu bukata ta musamman.
'Yan wasa nakasassu sama da 200 daga yankunan kasar 10 ne dai ke halartar gasar ta kwanaki 3, za kuma su fafata a wasanni da dama, da suka hada da goalball, da kwallon tebur, da kwallon Kwando da wasan Tenis da dai sauran su.