in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan ribar da Ghana ta samu daga zinariya da coco ta ragu
2014-02-14 15:52:47 cri

Bisa labarin da wani shafin Internet na kasar Ghana ya fitar a ranar 13 ga wata,, an ce sakamakon saukar farashinsu a shekarar 2013, baya ga man fetur, yawan kudin shigar da Ghana ta samu daga zinariya da coco ya ragu da kimanin dalar Amurka biliyan 1.3.

Bisa wannan rahoto an ce daga shekarar 2011, farashin coco ya ragu da kashi 20 cikin 100, yayin da farashin zinariya ya ragu da kashi 25 cikin 100.

A kwanan baya, mataimakin shugaban kasar Ghana Kwesi Bekoe Amissah-Arthur ya ce, yawan ribar da aka samu daga fitar da kayayyaki daga kasar ya sanya Ghana rage karfinta na shigar da kayayyaki, tare da kara fuskantar matsi ta fuskar ajiyar kudaden waje, har wa yau darajar kudin kasar wato Cedi ya ragu a cikin shekarar da ta gabata.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China