An ce dai wannan gobara ta tashi da misalin karfe 9 na safe, sannan kuma a kwashe sa'o'i da dama kafin aka kashe wajen da yamma. Wani babban jami'in hukumar kashe gobara ta kasar Ghana ya bayyana cewa, watalika yanayin zafi da iska mai karfi na daga cikin dalilan haddasa wannan gobara.
Ministan kiwon lafiya na kasar Ghana KwakuAgyeman-Mensah ya bayyana cewa, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar tana da isassun magunguna da za'a iyar yin amfani da su har zuwa tsawon watanni 3, don haka kadda jama'a su damu sosai dawannan lamarin.
An kafa hedkwatartawagar MDD ta musamman kan yaki da cutar Ebola a kasar Ghana, kana Ghana ita ce tashar zirga-zirga da kuma jigilar kayayyaki wajen yaki da cutar Ebola a yankin yammacin Afirka, kana cibiyar da gobara ta lalata ita ce ma'ajiyar magunguna mafi girma ta ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Ghana. (Zainab)