Shugabar jam'iyyar babban taron jama'ar kasar Ghana ta CPP Madam Samia Nkrumah ta bayyana cewa, ya kamata daukacin kasashen Afrika su koyi darussa daga kasar Sin wadda ta samu bunkasuwa cikin sauri.
Samia Nkrumah a zantawarta da manema labaru a ranar 1 ga wata ta ce, Ghana na bukatar bunkasa sana'ar kere-kere da daga karfin sarrafa kayayyaki ta yadda za a inganta karfin kasa na yin takara a duniya. Daukacin kasashe masu tasowa ciki hadda Ghana suna maida hankali a kan yadda tattalin arzikin kasar Sin ke bunkasuwa cikin sauri, kuma suna kokarin koyon abubuwa masu kyau daga kasar.
A ganin Samia Nkrumah, dalilin da ya sa Sin ta samu bunkasuwa mai kyau shi ne bin hanyar samun bunkasuwa da ta dogara da kanta bisa halin da Sin take ciki, abin da ya kamata jama'ar kasashen Afrika su yi koyi. (Amina)