in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana da Togo zusu kafa wata tashar binciken kan iyaka ta hadin gwiwa
2014-05-02 16:15:57 cri
Kasashen Ghana da Togo zasu fara aiwatar da wani shirin da ya shafi kafa wata tashar binciken kan iyaka ta hadin gwiwa, aikin da kungiyar tarayyar Turai ta zuba Euro miliyan 63.8 kansa, in ji ministar harkokin wajen kasar Ghana, madam Hanna Serwah.

Shirin ya shafi gina tashoshin binciken kan iyaka guda hudu tsakanin kasashen biyu, da zasu samar da wani yankin hadin gwiwa domin baiwa jami'ansu damar yin aiki.

Ministar kasar Ghana ta yi wadannan kalamai a yayin bikin watan dunkulewar shiyya, da kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS da tarayyar Afrika AU suka kaddamar.

Madam Serwah ta bayyana cewa wannan shiri na tashar binciken kan iyaka na hadin gwiwa tsakanin Ghana da Togo na cikin tunanin dunkulewar shiyyar dake hangen rage lokaci da jinkiri wajen ratsa kan iyakar kasashen biyu. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China