Wannan yarjejeniya za ta baiwa masu rike da fasfon diflomasiya ko na gwamnatin wadannan kasashe iznin shiga ko fita daga kasashen biyu ko yada zango a yankunan kasashen nasu ba tare da takardar Visa ba.
Jakadar Sin a kasar Ghana Sun Baohong da mataimakin ministan harkokin waje da hadewar yankuna na kasar Ghana Kwesi Quartey ne suka sanya hannun kan wannan yarjejeniya a madadin kasashen nasu.
A jawabinta Jakada Sun ta ce, sanya hannu kan wannan yarjejeniya wata babbar nasara ce wajen saukaka musaya tsakanin al'ummomin kasashen biyu,baya ga karfafa hadin gwiwa da abokantaka tsakanin Sin da kasar ta Ghana.
Shi ma a jawabinsa Mr Quartey ya ce,wannan yarjejeniya za ta kara zurfafa tare da daidaita kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Ghana da kasar Sin.(Ibrahim)