in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta bayar da fasahar sinadarin uranium da ba shi da wani inganci sosai
2014-03-06 15:19:12 cri

A ran 5 ga wata, kwamitin hukumar makamashin nukiliya ta duniya, wato IAEA ta amince kan yadda aka aiwatar da yarjejeniyar da aka daddale tsakanin Sin da Ghana a game da samar da yawan adadin sinadarin uranium din da ba shi da wani inganci sosai a tashar tace sinadarenta.

Bisa yarjejeniyar da aka daddale, an ce, Sin za ta bayar da fasahohin ga Ghana, domin taimakawa kasar wajen inganta karamar na'urar samar da karfin makamashi da na'urar za ta iya amfani da shi wajen samar da sinadarin uranium din da ba shi da wani inganci sosai tare da samawa kasar ta Ghana sinadarin uranium din da take bukata.

A halin da ake ciki dai, ana iya amfani da ingantattun sinadarin uranium a fannonin jama'a da kuma soja. Domin tabbatar da amfani da karfin nukiliya yadda ya kamata, kasashen duniya sun fara amfani da sinadarin uranium da ba shi da wani inganci sosai a maimakon sinadarin uranium mai inganci. Har kullum Sin ta goyi bayan kokarin da kasashen duniya ke yi wajen inganta tabbatar da amfani da karfin nukiliya yadda ya kamata, kuma ta yi alkawari a taron koli game da ba da tabbaci ga tsaron amfani da nukiliya da aka shirya a birnin Seoul cewa, tana son taimakawa dukkan kasashen da ke bukatar kyautata na'urar bincike ta sinadarin uranium mai inganci. Wannan aiki da Sin ta gudanar na taimakawa Ghana ta kyautata na'urar bincikenta ta nulikiya ya zama daya daga cikin matakan da Sin ke dauka don cika alkawarin da ta yi a baya.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China