in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gayyaci Ghana halartar gasar U-17 ta kasashe 4 a Namibia
2014-04-09 15:54:21 cri

Kulob din matasa 'yan kasa da shekaru 17 na kasar Ghana, wanda aka fi sani da 'the Black Starlets', zai halarci wata gasar ta kuloblikan kasashe 4, da za ta gudana daga ranar 18 zuwa ta 21 a kasar Namibia.

Shugaban kwamiti mai kula da kulob din, mista Wilfred Parma, ya bayyana hakan ga manema labaru, inda ya ce kungiyarsa ta Black Starlets za ta kara da Afirka ta Kudu, Namibia, da kulob din kasar Jamus Westphalia, wanda ya kan halarci gasar da ake gudanarwa duk bayan shekaru biyu-biyu, bisa wata yarjejeniyar hadin gwiwar Jamus da kasar ta Namibia.

A cewar Wilfred, halartar wannan gasar zai sa 'yan wasan Ghana zama a cikin shiri, kafin fara gasar share fagen babbar gasar 'yan kasa da shekaru 17 ta nahiyar Afirka dake tafe cikin watan Yulin shekarar 2015 mai zuwa.

Za dai a gudanar da wannan gasa ne, tsakanin kasashen 4 a filin wasan Swakopmund na kasar Namibia, da nufin baiwa 'yan wasa matasa damar fahimtar yanayin manyan gasanni na kasa da kasa, in ji jami'ai masu karbar bakuncin gasar.

Yanzu din haka, kulob na Ghana ya samu damar tsallake wasannin zagayen farko, na share fagen babbar gasar matasa 'ya kasa da shekaru 17 ta nahiyar Afirka, wadda za ta gudana a kasar Nijar a shekara mai zuwa, kafin karawar za su yi ko dai da Kenya ko kuma Sudan ta Kudu, a zagaye na 2 na neman damar ci gaba a wannan gasa.

A shekarar 2013 da ta gabata, yayin gasar 'yan kasa da shekaru 17 da ta gudana a Morocco, kulob din na Black Starlets bai samu damar tsallake zagayen farko ba. Amma a wannan karo, shugaban kwamiti mai kula da kulob din Wilfred Parma, yana sa ran ganin kulob dinsa ya samu babbar nasara, bisa la'akari da damar bude ido, da samun karin fasahohi da 'yan wasan kungiyar za su samu daga gasar da za a yi a kasar ta Namibiya, gabanin fara wasannin share fagen gasar 'yan kasa da shekaru 17 ta nahiyar Afirka a watan Yuli.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China