Da ya ke jawabi a wurin shugaba Mahama ya bayyana godiya kan yadda kamfanonin Sin suka taimakawa kasar Ghana wajen kammala wannan aiki mai inganci na samar da ruwa wanda ya taimaka wajen kyautata rayuwar jama'ar kasar Ghana.
An fara gudanar da aikin fadada samar da ruwa na Kpong dake da tazarar kilomita 54 daga arewacin birnin Tema ne a shekarar 2011, inda ake fatan bayan da aka kammala aikin zai samar da ruwa da ya kai ton dubu 186 a kowace rana inda zai zama wurin samar da ruwa mafi girma a kasar Ghana. (Zainab)