Rukunin ya gudanar da taron manema labaru karo na farko a ranar 31 ga watan Yuli da safe, inda aka bayyana cewa, kasar Ghana za ta sa ido sosai kan cutar Ebola. Shugaban sashen sa ido kan cututtuka na hukumar kiwon lafiya ta kasar Ghana ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu, akwai mutane 24 da ake ganin sun kamu da cutar Ebola a kasar, amma a karshe a gane ba haka ba ne.
Ministan kiwon lafiya na kasar Ghana Mensah ya bayyana cewa, kasarsa ta shirya kafa cibiyar rigakafi da bada jinya ga cutar Ebola, kuma ana bukatar dukkan asibitocin kasar da su bude dakin killatacce, ya yi bayanin cewa, an bude tsarin sa ido a birane 14 da mutanen waje suke shiga kasar Ghana don sa ido ga dukkan mutane da suka shiga kasar. (Zainab)