Wata sanarwar da aka rabawa manema labaru, ta ruwaito Annan na cewa wajibi ne a magance irin matsalolin da aka fuskanta yayin zaben da ya gabata, tare kuma da yin cikakken garambawul ga tsarin zaben kasar, domin samun karbabben zabe da kowa zai yi amana da shi.
Baya ga taya shugaba Mahama murnar samun nasara da tsohon magatakardar MDD ya yi, a hannu guda ya kuma yabawa babbar kotun kasar bisa kokarinta na tantance dukkanin bayanan da aka gabatar mata kafin yanke hukuncin shari'ar.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai babbar kotun kasar ta Ghana ta sallami kasar da dan takara, da makarraban jam'iyyar adawa NPP suka shigar, ta kuma tabbatar da shugaba Mahama a matsayin halastaccen shugaban kasar ta Ghana, wanda kuma zai ja ragamar kasar zuwa wasu shekaru 4 masu zuwa. (Saminu Alhassan)