in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Sin zai ware dala miliyan 100 don kafa masana'antar kera motoci a Ghana
2014-09-15 14:29:31 cri
Kamfanin dillancin labaru na kasar Ghana ya ce kamfanin samar da manyan motoci na kasar Sin mai suna Hubei Dali, na shirin ware dalar zunzurutin kudi har dalar Amurka miliyan 100, domin kafa wata masana'antar kera motoci a kasar ta Ghana.

Labarin ya nuna cewa, kamfanin na Hubei Dali ya sanar da hakan ne yayin da shugabannin sa ke ganawa da wasu jami'an kasar ta Ghana, a wani taron janyo ra'ayin masu zuba jari karo na 18 da ya gudana a birnin Xia'men dake gabashin kasar Sin.

A cewar shugabannin hukumar inganta aikin fidda kayayyaki zuwa kasashen waje ta kasar Ghana, an samu sakamako sosai bisa shawarwarin da ake yi da kamfanin na Hubei Dali, kana nan gaba kadan za a tura wasu jami'an kasar domin tattauna da tawagar kamfanin kan ainihin hanyar da za a bi wajen kafa wannan masana'anta, musamman ganin yadda janyo jarin waje a kasar ya dace da yunkurin gwamnatin kasar na kara samar da guraben ayyukan yi.

An dai kafa kamfanin Hubei Dali ne a shekarar 2010, kamfanin da kuma ke samar da kaso 5 bisa dari na motoci masu jigilar dalibai a nan kasar Sin. Ban da wannan kamfani, shi ma wani kamfani mai suna Guangzhou Automobile Group na nan kasar Sin, ya nuna sha'awar zuba jari a kasar ta Ghana, a dai wannan fanni na kafa masana'antar kera motoci.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China