in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Ghana ya bayyana kyakkyawan fata game da shiga sabuwar shekarar 2015
2015-01-01 16:08:43 cri
Shugaba Dramani Mahama na kasar Ghana, ya bayyana kyakkyawan fata, da hasashen cimma nasarori cikin sabuwar shekarar nan ta 2015.

Shugaba Mahama wanda ya bayyana hakan cikin sakon sabuwar shekara ga al'ummar kasar ta Ghana, ya bukaci daukacin jama'ar kasar da su fuskanci wannan shekara da kwarin gwiwa. Ya ce kamata ya yi dukkanin al'ummar kasa su hada karfi da karfe wajen cimma burin bunkasa kasa.

Shugaba Muhama ya kara da cewa shekarar da ta gabata na cike da kalubale da darussa, masu nunawa duniya muhimmancin rayuwar bil'adama. Kaza lika a cewarsa akwai alaka mai karfi tsakanin rayuwar al'ummar Ghana, da ta sauran kasashen Afirka, wanda hakan ke dada baiwa Ghanan wani matsayi mai muhimmanci.

Shugaban na Ghana ya kuma bayyana irin kokarin da kasarsa ta yi, na kasancewa a sahun farko, na kasashen da suka ba da cikakkiyar gudummawa ga kasashen Afrika, wadanda suka fuskanci annobar Ebola.

Ya ce shekarar 2014, shekara ce mai cike da kalubaloli, amma a daya hannun an cimma nasarar dakile da dama daga cikinsu, sakamakon kwazo da jan hali da aka nuna.

Daga nan sai ya alkawarta ci gaba da gudanar da budaddiyar gwamnati, wadda 'yan kasa za su iya tofa albarkacin bakinsu, a gabar da kasar ta Ghana ke ci gaba da aiwatar da managartan sauye-sauye. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China