Kasar Sin ta yi tir da harin da aka kai a birnin Paris na kasar Faransa a ran 7 ga wata, tare da mika ta'aziyyar ta ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu cikin lamarin.
Ta bakin kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar, Hong Lei da yayi bayani ga manema labarai a ranar alhamis din nan 8 ga wata a nan birnin Beijing ya ce, da kakkausar murya Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kai a wannan karo.
Yace dangane da hakan kasar ta nuna juyayi sosai ga iyalan mamatan tare da jaddada matsayinta na yaki da duk wani irin aikin ta'addanci da za a aikata, sannan tana goyon bayan kokarin da kasar Faransa ke aiwatar don kiyaye moriyar kasa.
Ban da haka kuma, Mr Hong ya ce, ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya riga ya buga ma takwaransa na Faransa Laurent Fabius wayar tarho don jajenta masa tare da nanata matsayin da Sin ke dauka na yaki da ta'addanci. (Amina)