in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari kan cibiyar mujallar Charlie Hebdo dake birnin Paris na kasar Faransa
2015-01-08 10:51:05 cri
A jiya ne wasu mahara suka kai hari kan cibiyar mujallar Charlie Hebdo dake birnin Paris na kasar Faransa, wanda ya haddasa mutuwar mutane 12 kana wasu mutane suka ji rauni. Bayan abkuwar lamarin, kasashen duniya sun yi Allah wadai da harin na wannan rana.

Shugaban kasar Faransa François Hollande ya sanar a daren ranar 7 ga wata cewa, kasar Faransa za ta yi zaman makoki har na tsawon kwanaki 3 a dukkan fadin kasar, a yayin za a sassauto da tutocin kasar zuwa kasa kasa don nuna jujayi ga mutanen da suka mutu a sakamakon harin. A halin yanzu, ba a kama wadanda suka kai harin ba, kana babu wata kungiya da ta sanar da daukar alhakin harin .

Kasashen duniya sun yi Allah wadai da lamarin, yayin da kwamitin sulhu na MDD ya bayar da sanarwa a ranar 7 ga wata, inda ya yi tir da harin da aka kai kan cibiyar mujallar ta Charlie Hebdo dake birnin Paris na kasar Faransa, wanda ya bayyana shi a matsayin mugun harin ta'addanci.

Kakalin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ya bayyana a wannan rana cewa, Sin ta yi Allah wadai da harin, kana tana adawa da duk wani nau'in ta'addanci, tana kuma goyon bayan matakan da kasar Faransa ta ke dauka na tabbatar da tsaron kasar.

Bisa labarin da ya fitar a shafinsa na internet shugaban kasar Rasha Vlładimir Putin ya yi tir da lamarin, kana ya jaddada cewa, kasar Rasha za ta ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasa da kasa don tinkarar barazanar ta'addanci.

Shi ma shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayar da sanarwa cewa, kasar Amurka za ta taimaka wajen ganin an kama wadanda suka kai harin. Obama ya bayyana cewa, Amurka da Faransa sun dade suna yaki da ta'addanci tare, don haka ya umurci hukumomin da abin ya shafa da su taimakawa kasar Faransa wajen ganin an kama wadanda suka kai harin.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China