in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira da a hada karfi domin kawar da ta'addanci
2013-07-18 10:42:16 cri
A ranar Laraba ne, kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yi kira da hada karfi tare domin kawar matsalar ta'addanci dake cigaba da kawo ja da baya a kasar Somaliya. Wakilin manzon musamman na kungiyar AU game da kasar Somaliya, Maharmat Saleh Annadif ya bayyana a yayin wani taro na kwanaki uku da aka shirya a birnin Mombasa na kasar Kenya dake gabar teku cewa ayyukan ta'addanci na ratsa iyakokin kasashe domin haka ya kamata a fuskance su bisa nazari.

Bayan nasarar da aka samu kansu, dakarun kungiyar Al-shebab sun canja wani salon yaki. Hanya mai kyau ta fuskantar wannan sabuwar matsala ita ce ta samun karfin tattara bayanai yadda ya kamata cikin lokaci in ji mista Annadif. Hukumomin tsaron kasar Somaliya wato sojoji, 'yan sanda da hukumar leken asiri da tattara bayanai, kasashen dake tallafawa kan sojoji da 'yan sanda da kuma wakilan kasashen Habasha, Sudan ta Kudu, Mali da Chadi sun amsa kiran wannan dandali na kwanaki uku. Hakazalika hukumar cigaban kasa da kasa (IGAD), AU, cibiyar bincike da nazarin ayyukan ta'addanci da ma cibiyar leken asiri da tattara bayanai da ayyukan tsaro a nahiyar Afrika sun halarci wannan taro.

Makasudin wannan haduwa shi ne na kafa da rike tsarin yin musanyar bayanai cikin lokaci tsakanin tawagar AU dake Somaliya, hukumomin tsaron kasar Somaliya da ma wasu muhimman hukumomin shiyya shiyya da ma nahiyar Afrika baki daya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China