Sakamakon harin na Larabar nan, mahukuntan kasar ta Faransa sun tsaurara matakan dakile karin hare-haren ta'addanci a birnin na Paris, musamman ganin cewa 'yan bindigar da suka aikata ta'asar sun tsere.
Yayin ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya auku, shugaba Francois Hollande, ya ce ko shakka babu harin ta'addanci ne aka kaddamar, a ofishin da da ma can ya sha fama da barazanar 'yan ta'adda. Matakin da ya sanya a baya aka tsananta tsaro a ofishin.
Shugaba Hollande ya sha alwashin cafke, tare da gurfanar da maharan gaban kuliya. Yana mai cewa kasar sa ta dade da kasancewa wuri, da masu tsauttsauran ra'ayin Islama ke hako, domin kaddamar da harin ramuwar gayya, bisa tallafin da take bayarwa wajen yakin da ake yi da dakarun kungiyoyin 'yan ta'adda a Iraqi, da kuma yankin Sahel na Afirka.