A kalla mutane goma ne suka rasa rayukansu, sakamakon wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a kauyen Tattaura na jihar Kaduna dake tsakiyar arewacin tarayyar Nigeriya.
Wata majiya ta tsaro ta ce, a yayin da aka kai farmakin misalin karfe 10 na dare a ranar Asabar, kamar yadda wadanda aka yi abin kan idonsu suka bayyana, bayan kisan mutanen goma, wasu mutane 5 sun samu munanan rauni, kuma nan take aka kai su babban asibitin Akwanga dake makwabciyar jihar Nasarawa.
Wata majiya ta jami'an tsaro, wadda ta nemi da a boye sunanta ta ce, al'ummar yankin dama su kan shirya raye-raye tsakanin yara, matasa da manya a lokacin bukukuwan kirismeti.
Shugaban karamar hukumar Nasiru Harande, wanda ya ba da tabbacin kai harin ya ce, harin da aka kai bai dace ba, kuma ya ce, wadanda suka kai harin sun sulale zuwa wadansu wurare.
Wani shugaban al'umma dake yankin Mike Sanga ya ce, an kai harin ne a wani kanti inda jama'a ke hutawa bayan sun kammala raye-raye. (Suwaiba)