Rundunar 'yan sandan jihar Kano a tarayyar Najeriya ta tabbatar da cewa, wasu mata 'yan kunar bakin wake sun kai harin bam a babbar kasuwar nan ta Kantin Kwari da ke birnin Kano.
Kwamishian 'yan sandan jihar Kano Adenrele Shinaba wanda ya tabbatar da abkuwar lamarin ga taron manema labarai ya ce, maharan sun rufe fuskokinsu da hijabi a lokacin da suka kai hare-haren yayin da kasuwar ke cike da mutane, inda bama-baman suka halaka maharan tare da wasu mutane guda 4.
Shi ma kakakin hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya (NEMA) Ezekiel Manzo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, masu aikin ceto da jami'an tsaro sun shiga aikin kwashe wadanda harin ya rutsa da su zuwa asibiti domin a yi musu magani, An kuma killace wurin da harin ya shafa don gudun aukuwar abin da zai biyo baya.
Kakakin ya ce, sama da mutane 29 ne aka garzaya da su asibitin kwararru na Murtala Mohammed da kuma Nasarawa sakamakon wadannan hare-hare. (Ibrahim)