in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya ba da umarnin bincike kan harin birnin Kano
2014-12-01 09:33:07 cri

Shugaba Goodluck Jonathan na tarayyar Najeriya, ya umarci jami'an tsaro da su gudanar da bincike na musamman, game da harin bam da aka kai babban masallacin Juma'a dake tsakiyar birnin Kano.

Rahotanni daga rundunar 'yan sanda sun tabbatar da rasuwar mutane 35, baya ga wasu 150 da suka jikkata, sakamakon wasu fashewa 3 da suka auku a ranar Juma'a.

Wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu kwafi, ta natata kudurin shugaban kasar na tabbatar da kawo karshen hare-haren ta'addanci da ake kaddamarwa kan jama'ar kasar. Shugaban Najeriyar wanda ya bayyana ayyukan ta'addanci a matsayin mugun hali na rashin imani, ya kuma mika sakon ta'aziyyarsa ga jihar Kano, da ma daukacin al'ummarta.

Kaza lika ya kara kira ga al'ummar kasar da su dada sanya ido tare da hada gwiwa da jami'an tsaro, domin kaiwa ga cimma nasarar yakin da ake yi da ta'addanci a kasar.

Kawo yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari, sai dai wasu na zargin kungiyar nan ta Boko Haram, wadda ta sha kai makamantan wadannan hare-hare a sassan arewacin kasar, ciki hadda jihar ta Kano.

Boko Haram dai na kaddamar da hare-hare kusan a kullum musamman a yankunan arewa maso gabashin kasar, tun bayan da sojoji suka fara matsa kaimin yakarsu a bara. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China