in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Birtaniya ta bankado shirin harin ta'addanci
2014-10-08 15:03:25 cri
'Yan sandan Birtaniya da hukumar leken asirin kasar sun dauki matakai a ranar Talatan nan 7 ga wata, inda suka bankado wani shiri na kai harin ta'addanci wanda ke da alaka da kunigyar masu tsattsauran ra'ayi na ISIS.

Hakan ya zama karo na farko da 'yan sandan kasar suka murkushe wani yunkurin kai harin ta'addanci da ya shafi kungiyar ISIS. A kokarin daidaita batun ne, 'yan sanda suka kama wasu samari 4 wadanda shekarunsu a duniya suka fi 20. An ce daya daga cikinsu ya koma Birtaniya daga kasar Syria kwanan nan, inda yake kulla shirin kai farmaki irin na ta'addanci a titunan birnin London. Kana wasu alamu sun sheda yadda suke shirin yayyanka kan mutane ko kuma kai hari ga jama'a da bindiga. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China