in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hare-haren bam sun halaka mutane 6 a Libya
2014-11-13 10:23:38 cri

Rahotanni daga Libya na cewa, wasu hare-haren bam da aka kai da mota a garuruwan kasar Libya sun halaka mutane 6, tare da jikkata a kalla 20.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar, ya bayyana cewa, harin farko ya faru ne ranar Laraba a garin Tobruk, hedkwatar majalisar dokokin wucin gadin kasar, yayin da hari na biyu ya faru a kusa da filin saukar jiragen saman soji na Labraq da ke gabashin birnin Bayda wato fadar gwamnatin rikon kwaryar kasar, sai dai ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wadannan hare-hare.

Wata majiyar asibiti ta bayyana cewa, wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a birnin Tobruk sun halaka mutum guda, tare da jikkata wasu mutane 20, kuma hudu daga cikinsu na cikin hali mai tsanani.

Bugu da kari, wani bam da aka dana a cikin wata mota ya tarwatse a kusa da filin saukar jiragen sama na soji da ke Bayda, inda nan ma ya halaka sojoji 5, baya ga wasu sojojin 2 da aka bayar da rahoton sun mutu tun farko, kana wasu 3 suka jikkata sanadiyar fashewar.

A ranar Lahadi ma wasu tagwayen bama-bamai sun fashe a birnin na Bayda, lokacin da firaministan kasar ta Libya Abdullah Al-Thinni ke ganawa da manzon MDD da ke Libya Bernardino Leon, ko da ya ke ba a bayar da rahoton wanda ya jikkata ba.

Tun lokacin da masu dauke da makamai suka kwace iko da birnin Tripoli a watan Agustan da ya gabata, gwamnatin rikon kwaryar kasar ta kaura zuwa birnin Bayda, yayin da sabuwar majalisar dokokin da aka zaba ke nata zaman a birnin Tobruk da ke gabashin kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China