A kalla yayan kungiyar musulunci ta Shi'a 30 ne suka rasa rayukansu a sakamakon wani harin kunar bakin wake, da aka kai a kan yayan kungiyar Shi'a, a yayin da suke tafiya a cikin jerin gwano a Potiskum na jihar Yobe dake arewa maso gabashin Nigeria.
Sakataren zartaswar hukumar gudanarwa ta asibitocin jihar Yobe Mamman Mohammed ya ce, kawo ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane a kalla 30, kana wasu mutane 89 sun samu raunuka.
Sakataren zartaswar ya bayyana hakan ne a yayin da yake yin bayani ga gwamnan jihar Yobe Ibrahim Gaidam, wanda ya kai ziyara ga wadanda harin ya rutsa da su a babban asibitin Potiskum, kuma ya ce, kawo ya zuwa yanzu wadanda suka samu munanan raunuka, an tura su zuwa wasu asibitoci dake wajen Potiskum a Azare da Nguru.
Gwamnan na jihar Yobe ya ba da umurnin da a bai wa wadanda harin ya rutsa da su kulawa kyauta, a inda ya bayyana cewar, gwamnati za ta biya duk kulawar da za'a yi musu.
Gwamnan ya mika ta'aziyarsa ga kungiyar musulmi ta Shi'a reshen jihar Yobe. (Suwaiba)