in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata 'yar kunar bakin wake ta kai hari a Najeriya
2014-11-13 10:33:48 cri

Majiyoyin tsaro a Najeriya sun tabbatar da cewa, wata 'yar kunar wake ta halaka lokacin da ta yi kokarin tayar da bam din da ke jikinta.

Lamarin ya faru ne a kwalejin ilimi na tarayya da ke garin Kontagora a jihar Niger da ke tsakiyar Najeriya, inda 'yar kunar bakin waken ta yi kokarin tayar da bam din a kusa da dakin karatun kwalejin.

Shugaban kwalejin Nathaniel Daniel ya shaidawa manema labarai cewa, 'yar kunar bakin waken ta kone kurmus, sannan dalibai da dama sun jikkata. Sai dai bai yi wani karon haske game da lamarin ba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ibrahim Gambari ya ce, rundunar ta tura masu kwance bama-bamai zuwa wurin da lamarin ya faru baya ga killace wurin da aka yi. Kuma har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin na Kontagora wanda ke zuwa kwanaki biyu kacal bayan da wani 'dan kunar bakin wake na halaka kansa ranar Litinin a wata makarantar sakandare da ke jihar Yobe mai fama da rikicin Boko Haram, da nan ma dalibai da dama suka mutu, kana wasu suka jikkata. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China