in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yar kunar bakin wake ta hallaka mutane a Bauchin Najeriya
2014-11-17 10:13:41 cri

A Najeriya, wata 'yar kunar bakin wake ta hallaka kanta, tare da wasu mutane a kalla 8, bayan da ta tada wani bam dake jikinta a wata kasuwa dake garin Azauren jihar Bauchi.

Shaidun gani da ido dai sun ce, harin na yamman ranar Lahadi ya kuma raunata mutane da dama, wadanda a yanzu haka ke samun kulawar jami'an lafiya. Tuni kuma aka garzaya da gawawwakin wadanda suka rasu zuwa asibitin koyarwa dake garin.

Wannan hari dai na zuwa ne kwanaki 5 bayan da wata 'yar kunar bakin waken ta hallaka kanta, yayin da take kokarin kaddamar da wani hari a kwalejin ilimi dake garin Kontagoran jihar Naija.

Yanzu haka dai, an tsaurara matakan tsaro a garin na Azaure, a kokarin da jami'an tsaro ke yi na tabbatar da doka da oda. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China