Wasu 'yan bindiga sun kaddamar da farmaki a kan wata makaranta a jihar Nijar dake tsakiyar Najeriya, a inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi, hakan ya haddasa dakatar da koyarwa a makarantar.
Wata majiyar 'yan sandan jihar ta Niger ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, 'yan bindia wadanda har yanzu ba'a san su waye ba, sun kutsa makarantar firamare da sakandare dake Limawa a birnin Minna, fadar gwamnatin jihar Nijar.
Kakakin 'yan sandan na Jihar Neja Ibrahim Gambari ya ce, lamarin ya wakana a daidai karfe 10 da rabi na safiyar Litinin a yayin da dalibai ke daukar darussa a azuzuwansu.
Ismail Bello, wanda aka yi abin kan idonsa ya ce, 'yan bindiga bayan da suka shiga makarantar sun yi ta harba bindiga barkatai, kuma daga baya suka yi amfani da takubba wajen raunata dalibai, hakan ya sa yara da yawa suka ji mummunan rauni.
Harin na ranar Litinin ya biyo bayan wani hari da aka kai kwanaki 6 da suka wuce a wata makarantar kwalejin ilmi ta gwamnatin tarayyar dake Kontagora a jihar ta Nijar. (Suwaiba)