in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana kudurinta na yakar ta'addanci
2014-05-22 20:15:34 cri
Bayan wani harin ta'addanci na baya-bayan nan da aka kai a arewa maso yammacin kasar Sin a ranar Alhamis da ya yi sanadiyar halaka mutane 31 kana wasu 94 suka jikkata,kasar ta Sin ta fito karara tana bayyana cewa, tana da tabbaci da karfin yakar 'yan ta'adda a kasar.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hong Lei ne ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa kowace rana,inda ya ce, harin na yau, wata alama ce ta karuwar ayyukan ta'addanci da nuna kin jinin bil-adama,al'umma da kuma kin jinin wayewar kai wadanda ya kamata Sinawa da al'ummar duniya su yi allahwadai da su.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China