in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu ababen fashewa sun hallaka mutane 31 a garin Jos dake Najeriya
2014-12-12 09:31:31 cri

A kalla mutane 31 ne aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon fashewar wasu ababen da ake zaton bama bamai ne, a garin Jos ta jihar Plateaun Najeriya.

Wata majiyar gwamnati ta bayyana cewa, fashewar farko ta auku ne da misalin karfe 6 da rabi na yammacin jiya Alhamis, a wata maciyar abinci dake kusa da kasuwar Taminus, kafin daga bisani wani bam din ya sake tashi 'yan mintuna kadan bayan na farkon, a kan titin masallacin juma'a dake birnin.

Kasuwar Taminus dai na daya daga wuraren taruwar jama'a a birnin na Jos, kuma bam din na farko ya tashi ne yayin da ake daf da kammala hada-hadar kasuwancin ranar, lokacin da aka fi samun cikowar jama'a a kasuwar.

Da yake karin haske game da aukuwar lamari, mai magana da yawun gwamnatin jihar Pam Ayuba, ya ce, mai yiwuwa ne adadin mutanen da suka rasu ya karu, sakamakon munanan raunukan da wasu suka samu.

Shi kuwa kakakin rundunar 'yan sandan jihar Emmanuel Abu, cewa ya yi tuni aka aike da dakarun rundunar wuraren da lamarin ya auku, domin tantance halin da ake ciki, tare kuma da ceton rayukan wadanda hare-haren suka rutsa da su. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China