Tare da hadin gwiwwar muhukunar 'yan sanda da suka hada da na yanki mai cin gashin kanshi na Xinjiang Uygur dake arewa maso yammacin kasar Sin,'yan sanda birnin Beijing sun kame wadanda ake zargi da hannu a ciki su biyar,kamar yadda kakakin 'yan sanda birnin Beijing ya sanar a ranar laraban nan.
Usmen Hasan da mahaifiyarsa da kuma matar sa sune a cikin motar kirar jeep mai lamba yankin Xinjiang wanda ya afkawa mutane a filin Tian'anmen da a take mutane biyu suka mutu sannan wasu 40 suka raunana,inji kakakin.
Su ma mutanen uku dake cikin motar jeep din sun mutu bayan da suka sa ma kansu wuta. (Fatimah Jibril)