in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta zartas da yarjeniyoyin tusa keyar wadanda suka aikata laifi tsakanin Sin da Afghanistan da Iran
2014-12-29 10:47:01 cri
Taron karo na 12 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin ya zartas da yarjeniyoyin tusa keyar wadanda suka aikata laifi tsakaninta da kasashen Afghanistan da Iran a ran 28 ga wata.

Ta hakan, yawan kasashen da suka sanya hannu kan irin wannan yarjejeniya tare da kasar Sin ya kai 36, ciki hadda Austriliya, Faransa, Korea ta kudu, Italiya, Spanish, Portugal da dai sauransu, abin da ya samar da ka'idar shari'a da doka da za a bi wajen tusa keyar wadanda suka aikata laifi tsakanin kasa da kasa, da kuma kiyaye moriyar kasar Sin.

Idan ba a manta ba, taron karo na 19 na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya zartas da dokar tusa keyar wadanda suka aikata laifi, matakin da ya baiwa kasar Sin damar toshe gibin shari'arta a fannin tusa keyar wadanda suka aikata laifi daga kasar Sin.

Ban da haka kuma, Sin ta kulla irin wadannan yajeniyoyi tare da kasashe da dama don hada kai da sauran kasashe da tabbatar da aikin shari'a a wannan fanni. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China