in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a kawo karshen dokar ta bace a Masar
2013-11-13 12:48:45 cri

Kakakin gwamnatin kasar Masar ya sanar a ranar Talata cewa, gwamnatin kasar tana dukufa wajen aiwatar da matakin wata kotu na kawo karshen dokar ta bace a kasar Masar, a wani labari da kamfanin dillancin labarai na MENA ya rawaito.

Sanarwar ta kakakin ta biyo bayan wata kotu ta ba da umurnin kawo karshen dokar ta bace a ranar Talata maimakon ranar Alhamis, ranar da gwamnatin kasar ya sanar da farko. Matakin na kotu ya kamata ya fara aiki ba tare da wani jinkiri ba, in ji MENA yayin da rawaito kalaman wannan jami'i. Gwamnatin kasar Masar na cikin jiran takardar matakin na kotun shari'a dake kawo karshen dokar ta bacen, in ji wata majiyar gwamnatin kasar a ranar Talata.

Kotun shari'ar ta fitar shari'ar da ta yanke a ranar Talata domin kawo karshen wannan lokaci na dokar ta bace a kasar ta Masar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China