1108murtala.m4a
|
A ranar Alhamis 7 ga wata ne, 'yan majalisar dokokin tarayyar Najeriya suka amince da bukatar da shugaban kasar Goodluck Ebele Jonathan ya gabatar musu na kara lokacin dokar-ta-baci a jihohin Borno, Yobe da kuma Adamawa dake arewa maso gabashin kasar da watanni shida, tare da zummar yaki da masu ta da zaune-tsaye.
'Yan majalisar dokokin sun jefa kuri'a ne ba tare da bayyana sunayensu ba, inda baki dayansu suka amince da bukatar da shugaba Jonathan ya gabatar.
A watan Mayu na wannan shekara ne, shugaba Jonathan ya sanar da kafa dokar-ta-baci a jihohin uku, a wani matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na magance hare-haren dake faruwa a yankin, wanda sanadiyyar haka aka tura dubban sojoji zuwa yankin tare da jiragen yaki masu saukar ungulu.
Tuni a ranar Laraba, a cikin wata wasikar da Mr Jonathan ya gabatar, ya ce sojojin Najeriya sun samu nasarori a kan 'yan bindigar yankin, sai dai akwai kalubalen tsaron da yake bukatar a murkushe shi.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga birnin Ikko, Najeriya.