in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Libya ta amince da sabuwar dokar zabe
2014-03-31 14:19:16 cri

A ranar Lahadin jiya ne, 'yayan babbar majalisar kasa ta Libya, suka amince da dokar zaben majalisar wakilai ta kasar.

Kakakin babbar majalisar kasar, Omar Hmaidan ya ce, mambobin majalisar, sun amince da dokar zaben majalisar wakilan ne, domin majalisar wakilan ta maye gurbin babbar majalisar kasar ta Libya tare da zama babbar majalisar koli, mai zayyana dokoki a lokacin wucin gadi na mulkin kasar.

An dai amince da wannan dokar ne da rinjayen kuri'u 124 daga cikin kuri'u 136 da aka kada.

A tsakiyar watan Fabrairu ne, babbar majalisar kasar ta yanke shawarar mika ikon da take da shi, a hannun majalisar wakilai, wacce aka shirya zaba, a nan gaba.

Kamar dai yadda tsarin mulkin kasar ya umurta, an baiwa babbar majalisar kasar ta Libya ikon rike mulkin kasar, har zuwa tsawon watanni 18, tun daga watan Agustar shekarar 2012, kuma a bisa tsarin dokar rikon kwaryar, ya zama tilas a kan babbar majalisar kasar, da ta mika mulki kafin 7 ga watan Fabrairu na shekarar 2014.

To amma an samu tsaiwata mika mulkin har zuwa watan Disamban wannan shekarar ta 2014, sabili da cewar aka shiga yanayi na rashin tabbas saboda halin da aka shiga bayan yakin kasar ta Libya, wanda kuma wannan rashin mika mulki ya janyo ka ce na ce da adawa daga bangaren talakawan kasar da kungiyoyin jama'a. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China