Li Keqiang ya gabatar da ra'ayoyin kasar Sin biyar kan warware matsalar Afghanistan, wato a bari jama'ar Afghanistan su gudanar da harkokin kasa da kansu, da sa kaimi ga kokarin samun sulhu, da gaggauta sake raya tattalin arzikin kasa, da neman hanyar samun bunkasuwa da kuma kara yin amfani da taimakon da kasashen waje suke baiwa kasar
An tsara shirin Istanbul a shekarar 2011, wanda shi ne shirin hadin gwiwa daya kawai da kasashen da batun Afghanistan ya shafa suke jagoranta a halin yanzu. Wannan ne karo na farko da kasar Sin ta karbi bakuncin wannan taro, kana shi ne taro na farko da aka gudanar kan batun Afghanistan bayan da aka kafa sabuwar gwamnatin kasar, inda ministocin harkokin waje da wakilai na kasashe 14 dake cikin tsarin shirin Istanbul, da sauran kasashe 16, kungiyoyin kasa da kasa da wasu yankuna 12 suka halarci wannan taron. (Zainab)