in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci Afghanistan da ta gaggauwa yunkurin neman sulhu ta hanyar siyasa
2014-10-31 20:48:11 cri
A yayin taron ministocin harkokin waje na shirin Istanbul kan batun kasar Afghanistan karo na hudu a yau Jumma'a, ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya jaddada cewa, ya kamata a gaggauta yunkurin neman sulhu ta hanyar siyasa da kuma kyautata ayyukan tafiyar da harkokin kasar Afghanistan.

Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan kasar Afghanistan za ta gano wata hanyar bunkasuwa, wadda ta dace da yanayin kasar, moriyar jama'ar kasa wadda kuma ya samu amincewar al'ummar kasar baki daya kana ya samu goyon bayan gammayar kasa da kasa a yayin da aka samu sauyin siyasa a kasar, ta yadda za ta iya cimma burinta na mulkin kai da kuma biyan bukatun jama'arta.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta sanar da shirin ba da taimako da horaswa ga kasar Afghanistan, kuma za ta gudanar da aikin yadda ya kamata da ci gaba da yin hadin gwiwa da kasar Afghanistan kan harkokin dake shafar zaman rayuwar jama'ar kasa da dai sauransu, domin taimakawa kasar wajen samun ci gaba bisa karfin kanta ta yadda za ta iya samun dauwamammen ci gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China