Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya sanya hannu kan dokar nan ta surrunta bayanan jama'a, dokar da za ta baiwa 'yan kasar 'yancin surrunta bayanan da suka shafe su.
Kakakin fadar shugaban kasar Mac Maharaj ne ya tabbatar da hakan ranar Laraba, yana mai cewa, dokar, za ta bayar da damar surrutan bayanan da suka shafi jama'a yayin da sassan da abin ya shafa ke kokarin tantance su.
Bugu da kari, ana fatan dokar, za ta dai-daita batun 'yancin surrunta bayanai da sauran 'yanci, musamman 'yancin samun bayanai, da kuma muhimmancin kare muradun mutum, ciki har da 'yancin samun bayanai a ciki da sauran sassan kasar.
Wadannan 'yancin da dokar ke magana a kai, sun hada da 'yancin kariya daga tattara bayanai ko watsa su ba bisa ka'ida ba da kuma amfani da bayanan da suka shafi wani mutum.
Ya zuwa yanzu, majalisar dokokin kasar ta bullo da dokar da ta amince da bude wani ofishi mai zaman kansa da zai rika sa-ido kan yadda dokar ke aiki, a matsayin kafar cimma nasarar manufar kafa wannan doka. (Ibrahim)