in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta kara girke sojoji 1000 a Afghanistan
2014-12-07 17:50:44 cri
Ministan tsaron Amurka Chuck Hagel, ya ce adadin dakarun Amurka a kasar Afghanistan zai kai ga soji 10,800, wanda ya karu da kimanin dubu kwatankwacin da zarar an tura karin dakaru 1000yawan sojojin da kasar ta Amurka ta shirya girkewa a kasar a baya, karkashin sabon shirin da Amurkan ta kuduri niyyar aiwatarwa..

Chuck Hagel wanda ya bayyana hakan ya yin taron manema labaru, bayan ganawar sa da shugaban Afghanistan Ashraf Ghani, ya kuma bayyana cewa Amurka, ta daf da tura karin sojojin na shirin girke sojoji kiamnin 10, 800 bayan kmmalar shekarar nan ta 2014, domin ba da taimako wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar. Sai dai ya ce aikin sojojin na Amurka a Afghanistan ba zai canza ba, haka ma lokacin janye su daga kasar shi ma bai canza ba.

A baya dai shugaba Barack Obama ya bayyana burin kasar sa na jibge sojoji 9800 ne a kasar ta Afghanistan bayan shekarar nan ta 2014, kana an yi shirin janye wasu daga cikinsu kafin karshen shekarar 2016. Sai dai matsaloli masu nasaba da tsaro da Afghanistan din ke fuskanta, sun sanya shugaba Obaman sauya matsaya, inda ya amince da kara yawan sojojin Amurka a kasar, tare da amincewa da yakin da ake ci gaba da yi da kungiyar Taliban, da dai sauran batutuwa. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China