140228murtala-labari
|
Majalisar dokokin jihar Neja dake arewacin Najeriya, ta zartar da wata sabuwar doka, domin dakile mummunan laifin nan na fyade wanda ke neman zama ruwan dare a jihar.
Majalisar ta zartar da cewa duk wanda aka samu da laifin aikata fyade zai fuskanci hukuncin daurin shekaru 21 a kurkuku.
Kafin zartar da wannan sabuwar doka, ana yanke hukuncin dauri na tsahon shekaru 8 ne zuwa 14, kan wadanda aka samu da aikata wannan laifi.
Kakakin majalisar, Hon. Adamu Usman ya bayyana cewa, hukuncin dokar zai shafi duk wanda ya aikata fyaden, ko ya taimaka aka aikata hakan ta kowace irin siga.
Shi kuma shugaban kwamitin shari'a na majalisar, Hon. Isa Kawu, cewa ya yi burin dakile wannan matsala da ta ke addabar mata ce ta sa suka kafa dokar. Inda ya kara da cewa matsalar fyade matsala ce da ya kamata a dauke ta da muhimmanci, a kuma yi tunani mai zurfi a kan ta, saboda yadda take haifar da kaskanci ga mata.
Zuwa yanzu wasu kungiyoyin mata sun yi maraba da sabuwar dokar ta jihar Neja. Har ma Mary Jalingo, shugabar mata 'yan jarida ta yabawa majalisar, sa'annan ta yi kira ga mahukunta su tabbatar da aiwatar da dokar a kan duk wanda aka samu da laifin, don kar ta zama magana ta fatar baki kawai.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.