in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fitar da doka game da zanga-zanga a kasar Masar
2013-11-25 10:29:34 cri

Shugaban rikon kwarya na kasar Masar Adly Mansour, ya amince da wata doka da za ta daidaita yawon zanga-zangar da ke faruwa a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ta Masar (MENA) ne ya sanar da hakan a ranar Lahadi, inda ya ce, sanya hannu kan wannan doka, ta zo ne yayin da daliban jami'o'in kasar suka yi zanga-zanga a yankunan kasar da dama, don murnar cika kwanaki 100 da tarwatsa sansanonin masu bore guda biyu da jami'an tsaro suka yi, inda suke neman a maido da shugaban Mohamed Morsi da aka tumbuke daga mukaminsa.

Bisa tanadin dokar, daga yanzu duk masu son shirya taro, wajibi ne su rubutawa ma'aikatar cikin gidan kasar takarda kwanaki uku kafin ranar ganawar tasu. inda a ciki ake bukatar su yi bayani dalla-dalla game da dalilansu na shirya boren, bayanai game da masu shirya shi wannan taro, sannan za a duba taken da za su yi amfani da shi, wuri da kuma lokacin shirya wannan zanga-zanga.

Dokar ta ce, ma'aikatar harkokin cikin gidan tana da ikon soke zanga-zangar, sa'o'i 24 kafin a fara ta, idan har tana ganin zanga-zangar za ta iya kawo barazana ga harkokin tsaro da dokar kasa, kuma za ta iya canja wuri ko dalilin shirya macin.

Bugu da kari, dokar ta zayyana cewa, idan har masu shirya boren suka ki amincewa da matakin da ma'aikatar harkokin cikin gidan ta dauka, suna iya daukaka kara a gaban kotun farko da za ta amsa bukatunsu cikin hanzari. Har ila yau, dokar ta haramta gudanar da tarukan siyasa a wuraren Ibada, ko yin maci daga ko zuwa wuraren Ibadan da yin taro a wuraren da jama'a ke dauke da makamai, ababan fashewa, da sauran abubuwan da ka iya zama hadari ga jama'a da gine-gine.

Kana daga karshe, dokar ta kuma haramta sanya abubuwan boye fuska a yayin zanga-zanga. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China