in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar za ta soke dokar ta bace a ranar yau Alhamis
2013-11-14 10:16:15 cri

Hukumomin wucin gadi na kasar Masar za su kawo karshen dokar ta bace a ranar yau Alhamis tun bayan aiwatar da wannan doka yau da kusan watanni uku da suka gabata, in ji wani labari da kamfanin dillancin labarai na kasar MENA ya rawaito a ranar Laraba tare da ambato kalaman wata majiyar gwamnatin wannan kasa.

Wata kotun kasar ce ta ba da umurni a ranar Talata wato za a kawo karshen wannan dokar ta bacen tun ma ranar ta Talata maimakon ranar ta Alhamis da aka tsaida. Amma duk da haka, jami'an tsaron sun cigaba da amfani da wannan doka a ranakun Talata da Laraba, tare da ba da hujjar cewa, ba su samu wannan mataki ba daga wajen kotun.

Ministan dake kula da harkokin hukumomi Hany Mahmoud ya bayyana cewa, har yanzu gwamnati ba ta samu takardar wannan mataki ba daga kuto, a cewar MENA.

Gwamnatin dai ta wucin gadi a kasar Masar ta sanar da kafa dokar ta bacen a ranar 14 ga watan Agustan da ya gabata a yayin da jami'an tsaro suka tarwatsa wasu tarurukan gangami biyu na magoya bayan Mohamed Morsi a biranen Alkahira da Gizeh. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China