A yayin taron, an gabatar da cewa, babban burin da kasar Sin take son cimmawa shi ne kafa tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin dangane da tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka, da kuma raya kasar Sin ta gurguzu ta yadda za ta zama wata kasa da ke tafiyar da harkoki bisa doka. Har wa yau an bukaci a kammala wasu muhimman ayyuka, wadanda suka hada da kyautata tsarin dokoki na gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin wanda ke ba da fifiko ga tsarin mulkin kasa, inganta aiwatar da tsarin mulkin kasa, zurfafa gudanar da harkokin gwamnati bisa doka, tabbatar da doka ta yin aiki cikin adalci, sa kaimi kan raya zaman al'ummar kasa da ke aiwatar da doka yadda ya kamata, kara wa ma'aikatar aiwatar da dokoki karin karfi, da inganta da kyautata shugabancin da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin take yi wajen kara azama kan tafiyar da harkokin mulkinkasa bisa doka daga dukkan fannoni.
Haka zalika, an jaddada a yayin taron cewa,muddin ana bukatar jajircewa kan tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka, da farko wajibi ne a nace ga tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa tsarin mulkin kasa. Sannan idan har ana bukatar nacewa kan mulkin kasa bisa doka, to, dole a nace ga tafiyar da mulkin kasa bisa tsarin mulkin kasa. Don haka ya zama wajibi a kyautata tsarin gudanar da tsarin mulkin kasa da sa ido a kai, da tsarin Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da zaunannen kwamitinta na sa ido kan tsarin mulkin kasa, da kuma tsarin ayyukan yin bayani kan tsarin mulkin kasa.