Cikin wannan daftarin dokar an mai da hankali kan karfafa ikon jama'a, da wasu kungiyoyin kasa wajen daukaka kara, da nufin kiyaye hakkokin al'umma ta hanyar dokoki yadda ya kamata.
Don gane da hakan, wasu masana na ganin cewa an gyara dokar ne don karfafa aikin sa ido kan hukumomi masu alaka da gudanar da mulkin kasa, ta hanyar yin amfani da wannan doka ta gabatar da kararraki. Haka zalika daftarin ya tanaji karfafa hanyoyin kiyaye hakkin jama'a, da wasu kungiyoyin kasa yadda ya kamata. (Maryam)