Mambobin kwamitin sulhu na MDD, sun cimma matsaya guda game da wani kudurin dake tabbatar da goyon bayan su ga kasar Afganistan.
Kudurin wanda aka amince da shi bayan kada wata kuri'a a zauren majalissar, ya kuma jaddada cewa rundunar hadakar kasashen duniya a Afganistan wadda ke gudanar da ayyukan tallafi karkashin MDD, za ta kammala aikin ta a karshen wannan shekara da muke ciki.
Har wa yau kudurin ya bayyana bukatar dake akwai ga kasashen duniya, da su baiwa kasar ta Afghanistan dukkanin goyon bayan da ya dace, domin tabbatar da burin wanzar da zaman lafiya da aka sanya gaba.
Ban da wannan, kudurin ya nuna amincewar kwamitin, da kokarin da aka yi na kara karfin dakarun tsaron kasar, ya yin da kuma ake fatan kammala mika harkokin tsaron kasa yadda ya kamata a karshen shekarar nan ta 2014.
Ana kuma fatan nan gaba mahukuntan kasar zasu kai ga iya daukar dawainiyar tsaron kasar. Kwamitin tsaron ya kuma bukaci kasashen duniya, da su ci gaba da bada taimako cikin dogon lokaci, domin karfafa karfin soji da rundunar tsaron kasar.
Idan ba a manta ba dai, an kafa rundunar kasa da kasa ta tallafawa Afghanistan ne a shekarar 2001, bisa kudurin da kwamitin ya zartas. Kana a watan Oktobar bara, kwamitin ya zartas da kudurin baiwa rundunar iznin gudanar da ayyuka a daukacin kasar.
A cikin watan nan ne kuwa, kwamitin ya sanya ranar 31 ga watan Disambar nan, ta zamo ranar karshe ta aikin rundunar, inda za a mikawa gwamnatin kasar nauyin tsaron kasar baki daya. (Amina)