in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata kasashen Sin da Amurka su kara fahimtar juna lokacin da suke aiwatar da doka tare
2014-12-03 21:07:21 cri
A yau Laraba 3 ga watan Disamba, Mr. Liu Zhenmin, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasashen Sin da Amurka suna da moriya bai daya da karfin yin hadin gwiwa a fannin aiwatar da dokoki, sabili da haka, ya kamata su nemi moriya iri daya tsakaninsu, kokarin fahimtar juna da mai da hankali kan muradun juna, ta yadda za su amince da fadada sakamakon yin hadin gwiwa.

A yayin taro karo na 12 na rukunin mu'amalar harkokin aiwatar da dokoki cikin hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka da aka kaddamar yau da safe a nan Beijing, Liu Zhenmin ya ce, yanzu kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan matsayin tafiyar da harkokin mulkin kasa bisa doka, wato za ta ci gaba da kyautata tsarin dokoki dake dacewa da tsarin gurguzu na kasar Sin a gida, kuma za ta kara yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, ciki har da kasar Amurka a fannin aiwatar da doka.

A nasa bangaren, Mr. Daniel Kritenbrink, mataimakin shugaban ofishin jakadancin kasar Amurka dake nan kasar Sin ya bayyana cewa, yin mu'amala wani dandali ne da ya dace. Ya yi imani cewa, wannan dandali zai taka muhimmiyar rawa wajen kara bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu lami lafiya cikin hali mai dorewa. Yana kuma fatan sassan biyu za su kara yin musayar bayanai a lokacin da suke aiwatar da doka cikin hadin gwiwa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China