Mr. Ablakwa ya ce makarantun za su kasance a rufe, har ya zuwa lokacin da za a karfafa aikin tantance, da karfafa tsaron iyakokin kasar don hana shigar cutar.
Mataimakin ministan wanda ya bayyana hakan ta wata kafar radio dake birnin Accra, ya kara da cewa an samar da sahihin tsari na yiwa daliban kasashen Najeriya, da Liberia da na Saliyo masu karatu a kasar gwaji, kafin su shiga kasar.
Bugu da kari ya Ablakwa ya ce gwamnatin kasar ta na da shirin dakatar da gudanar da tarukan kasa da kasa da na al'umma, duka dai domin cimma burin da aka sanya gaba.
Daga nan sai ya tabbatar wa al'ummar kasar ta Ghana, shirin da gwamnati ke da shi, na tabbatar da kare yaduwar wannan cuta mai hadari ta Ebola a daukacin sassan kasar.