WHO ta amince da yin amfani da gwajin magani wajen yin jinya ga mutanen da suka kamu da cutar Ebola
Ya zuwa yanzu, ba a samu magunguna ko allurar rigakafi na cutar Ebola ba, amma an ce wasu mutanen da suka kamu da cutar Ebola sun karbi magungunan gwaji inda suka samu sauki a kwanakin baya. Game da wannan batu, hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta gudanar da taron ilmin likitoci don yin bincike kan rawar da irin magungunan gwaji ke taka wajen yin jinya ga cutar Ebola.
A ranar 12 ga wata, hukumar WHO ta gabatar da sakamakon binciken, inda aka ce, babu laifi na samar da magungunan gwaji ga mutanen da suka kamu da cutar Ebola. (Zainab)