in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dakatar da fasinjojin kasashe uku shiga kasar Gambia
2014-08-12 10:14:20 cri

Mahukuntan sashen sifirin jiragen saman kasar Gambia sun ce tun daga ranar Litinin, an dakatar da zirga-zirgar fasinjojin kasashen Liberia, da Saliyo da Guinea a kasar.

Hakan a cewar ofishin muhimmiyar doka ce da aka zartas domin hana bullar cutar nan ta Ebola a kasar. A cewar wani babban jami'in ofishin wanda bai amince a bayyana sunansa ba, duk da daukar wannan mataki zai sanya kasar asarar fasinjoji, a hannu guda hakan ya zama wajibi domin kare rayukan al'ummar kasa.

Wannan ne dai karo na biyu da Gambia ta dauki irin wannan mataki, inda cikin watan Afrilun da ya gabata ma, aka dakatar da daruruwan fasinjoji masu shirin tashi zuwa Saliyo, da Guinea, da kuma Liberia a filin jirgin birnin Banjul, bayan da mahukuntan kasar suka hana jiragen kasar daukar fasinjoji daga kasashen da ke fama da cutar Ebola.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China