Cibiyar ta ce an gudanar da bincike kan mutumin ne a asibitin Princess Margaret, kuma shi ne mutum na farko da aka zaci yana dauke da wannan cuta a kan hanyar sa ta zuwa Hong Kong, tun bayan da cutar ta barke a wasu kasashen yammacin Afirka.
An ce mutumin dan shekaru 32 da haihuwa ya nuna alamun cutar ta hanyar amai da gudawa, ya kuma isa Hong Kong a ranar Alhamis. Inda daga nan aka aike da shi zuwa asibiti.
Mutane sama da 900 ne dai suka rasa rayukan su bayan sun kamu da cutar ta Ebola a wasu kasashen dake yammacin Afirka.
Tuni kuma hukumar lafiya ta WHO ta ayyana wannan cuta a matsayin wata annoba ga duniya baki daya, wadda kuma duniya ba ta gamu da kamar ta ba cikin shekaru 40 da suka gabata.