Ministan kiwon lafiya na kasar Kamaru, Andre Mama Fouda, ya karyata a ranar Litinin da jita jitar dake bayyana cewa, an gano wasu mutanen dake dauke da kwayoyin cutar Ebola a Kamaru mai makwabtaka da Najeriya wanda ta sanar da kamuwar mutane goma kuma daga cikinsu biyu sun mutu.
Babu wani marasa lafiya dake fama da Ebola a Kamaru, in ji ministan kasar Kamaru a kan wata kafar CRTV, da yake maida martani kan jita jitar dake nuna cewa, asibitin Liquintinie dake birnin Daoula ya karbi wani mutumin guda dake fama da cutar Ebola. (Maman Ada)